fidelitybank

Har na cire raina da samun tikitin takara a 2023 – Tinubu

Date:

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana jin daɗi da godiyarsa ga ƴan Najeriya bisa addu’o’in da suka yi masa na cika shekara 73 a duniya.

Tinubu ya bayyana haka a taron buɗa- baki na musamman da ya jagoranta a fadar gwamnatin ƙasar a daren Asabar domin murnar zagayowar ranar haihuwarsa, kamar yadda mai magana da yawunsa, Bayo Onanuga ya bayyana a wata sanarwa.

Da yake jawabi kan fafatukar da ya sha kan zaɓensa na shekarar 2023, Tinubu ya ce sai da ya kusa haƙura da takarar baki ɗaya saboda ƙalubale.

“Waɗanda suke kusa da ni sai suka fara tunanin ba zan kai ga gaci ba. Wani daga cikinsu ya taɓa samuna, ya ce min yana neman naira dubu 50 ne zai saya wa wani kawunmu abinci. Ya ce min saboda ni babu tsabar kuɗi a gari, mutane suna ta wahalar neman tsabar kuɗi. Kuma kawunmu ɗin attajiri ne, amma ko naira 10,000 babu a hannunsa.

“Da na miƙa masa tsabar kuɗin naira 50,000, sai ya kalle ni ya ce min da wahala in samu nasara, ni kuma na ce masa zan samu nasara.”

Tinubu ya ce a lokacin ne jikinsa ya yi sanyi har ya fara tunanin ajiye takarar, “amma sai Aminu Masari ya ƙarfafa min gwiwa, ya ce ba matsala, kada in juya baya,” in ji shi.

Tinubu ya ƙara da cewa ya karɓi ƙasar ne a daidai lokacin da take fama da matsin tattalin arziki, “shi ya sa na yanke shawarar ɗaukar matakai masu tsauri tun a farko a mulki, ciki har cire tallafin man fetur wanda ba ya cikin asalin jawabin da zan yi.”

kano news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp