Shugaban mulkin sojin Nijar, Janar Abdourahamane Tchiani, ya sha alwashin cewa babu ɗaya daga cikin ƙasashen Sahel uku da suka yanke shawarar ficewa daga kungiyar raya tattalin arzikin kasashen Afirka ta yamma wato ECOWAS da za ta koma cikin ƙungiyar.
Janar Tchiani ya yi wannan jawabin ne a wata hira da ya yi da tashar labarai ta RTN a Yamai babban birnin ƙasar ranar Litinin.
Hukumomin soji a Burkina Faso da Mali da kuma Nijar a ranar 28 ga watan Janairu, sun sanar da ficewa daga kungiyar ECOWAS ta yammacin Afirka cikin gaggawa.
Shugabannin kasashen uku sun fitar da wata sanarwa, inda suka ce “shawarar da suka ɗauka ta barin ƙungiyar mai girma ce kuma ba tare da bata lokaci ba”.
“Saboda mu ‘yan kungiyar ne ya sa aka daina samar mana da abinci da magunguna. An kuma katse wutar lantarki kuma an hana mu taba kudadenmu. Don haka, muka tuntubi abokanmu na yankin Sahel kan ficewa daga kungiyar saboda inganta rayuwar ‘yan kasashenmu da cewa mu janye daga kungiyar da ke bin ra’ayoyin kasashen waje.Saboda haka mun janye mambanmu daga kungiyar kuma ba za mu taba komawa cikin kungiyar ba.” In ji Janar Tchiani.
Da yake mayar da martani kan sakamakon janyewar ƙasashen daga ƙungiyar Ecowas a kan harkokin tsaro da kasuwanci da zamantakewa, Tchiani ya kara da cewa “yanzu duniya a cure take wuri guda saboda haka ba sai da Ecowas kaɗai za mu rayu ba, don haka, Allah zai ciyar da kowane ɗan adam da ya halitta.”
Dangane kuma da batun hambararren shugaban kasar, Mohamed Bazoum, sai Janar Tchiani ya ce “ba za mu taba sakin Bazoum ba. Sakin Bazoum ya yi daidai da daɓa wa kanmu wuka a ciki wanda hakan zai cutar da ‘yan Nijar”.
Kungiyar ECOWAS dai ta sha nuna rashin amincewarta da ficewar kasashen, inda ta nemi da su bi hanyoyin da kungiyar ta shimfida na ficewa daga Ecowas bisa ka’aida kasancewar dukkan kasashen sun rattaba hannu kan yarjejeniyar.