Hukumar Zaɓe mai zaman Kanta INEC, ta bayyana matakan da za a bi domin kaɗa ƙuri’a a ranar zaɓe.
A wani saƙo da hukumar ta wallafa a shafinta na Tuwita ta bayyana matakai bakwai da ta ce za a bi domin kaɗa ƙuri’a ranar zaɓen.
A ranar 25 ga watan Fabrairun da muke ciki ne dai za a gudanar da zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisun dokokin ƙasar.
Matakin farko shi ne lokacin fara zaɓen wanda hukumar ta ce zai fara da misalin ƙarfe 8:30 na safe.
Mataki na biyu shi ne gabatar da katin zaɓe ga jami’an zaɓe domin tantance shi ta hanyar amfani da na’urar BVAS.
Daga nan sai a duba ko sunan mutum na cikin rajistar masu kaɗa ƙuri’a a wannan rumfar zaɓen.
Mataki na gaba shi ne na’urar BVAS za ta tantance mutum ta hanyar saka ɗan yatsarsa a jikinta, daga nan sai a bai wa mutum ƙuri’ar da zai kaɗa.
Sai matakin kaɗa ƙuri’a wanda hukumar ta ce ta ware wuri na musamman da za a shiga domin kaɗa ƙuri’ar a asirce.
Matakin ƙarshe shi ne bayan kaɗa ƙuri’a mutum zai bar rumfar zaɓen, ko ya yi nesa da rumfar zaɓen na akalla mita