Firaiministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya maida martani kan wadanda ya ce su na ƙoƙarin matsawa sojin kasarsa lamba kan matakan da suke dauka a Gaza.
Ya ce hanyar da ya dace ita ce amfani da karfi wajen murkushe Hamas.
Wannan na zuwa ne bayan Jami’an gwamnatin Amurka suka fara bayyana rashin gamsuwa kan matakan da Isra’ila ke ɗauka a yaƙin ta da Hamas.
Tun da fari Sojojin Isra’ila sun fara shirin ƙaddamar da yaƙi ta kasa a Khan Younis.
Sojojin Isra’ila sun sanar da isa tsakiyar Khan Younus, wannan ne wurin da Sojin Isra’ila sukai amanna mambobin Hamas ke fakewa.
Rahotanni sun ambato Netanyahu ya shaidawa ‘yan uwan wadanda suke hannun Hamas cewa abu ne mai matukar wuya a kubutar da su ahalin da ake ci