Masu zaɓe a Jamus sun fara hallara domin kaɗa ƙuri’arsu a zaɓen ƙasar bayan yaƙin neman zaɓe mai zafi da aka yi wanda batun koma-bayan tattalin arziƙin ƙasar da kuma wasu jerin hare-hare da aka yi suka sa bataun ɓaki da shige da fice suka ɗauki hankali sosai fiye da komai.
Friedrich Merz, mai shekara 69 kuma mai ra’ayin riƙau shi ne ake ganin zai iya yin nasara ya zama shugaban gwamnatin Jamus ɗin ta gaba, a wannan zaɓe da Amurka da Turai suka zuba wa ido.
Mista Merz ya yi alƙawarain gyara komai a cikin shekara huɗu – a ƙasar da ita ce mafi ƙarfin tattalin arziƙi a Turai, wadda kayayyakin jin daɗin jama’a suka yi baya.
Idan har jam’iyyar Merz wato Christian Democrats (CDU) ta yi nasara, to zai buƙaci ya yi haɗaka da aƙalla jam’iyya ɗaya, wataƙila ta Olaf Scholz, Social Democrats, wadda gwamnatinta ta ruguje a shekarar da ta wuce.