Gwamnan Jihar Ebonyi, ya ce, bai damu da hukuncin da kotu ta yi masa ba, na tsige shi daga kan kujerar sa.
Kotu ta tsige Umahi da mataimakinsa, Eric Igwe a kan sauya shekar su daga PDP zuwa APC.
Yayin bayani a ranar Laraba bayan kammala taro da Buhari, ya ce, bayan tsige shi, har kiba da kyau ya kara kamar yadda kowa ya ke gani.
David Umahi, gwamnan Jihar Ebonyi ya ce, bai damu da hukuncin da kotu ta yanke ba na kwanan nan wanda ta tsige shi daga mukaminsa na gwamna.