Sabuwar dokar takaita zirga-zirgar Babura masu ƙafa uku da aka fi sani da Adaidaita Sahu, ta rage matsalar fashi da makami da sace-sacen waya da sauran abubuwan da suka shafi zamantakewa.
Jihar Kano dai ta sha fama da yawaitar fashin dare, fashin gidaje, da sauran laifuffukan da suka shafi masu amfani da babur uku daga karfe shida na safe zuwa karfe 10 na dare.
Da yake zantawa da manema labarai kan dokar, babban daraktan hukumar kula da zirga-zirgar ababen hawa ta jihar Kano KAROTA, Baffa Babba DanAgundi, a ranar Alhamis, ya ce, an samu raguwar masu aikata laifuka a jihar bayan haramcin ta.
Ya ce, “duk da cewa binciken da muka yi ya nuna cewa ɗimbin Ma’aikatan babur waɗanda ke gudanar da ayyukansu bisa manufa ta doka.
Baffa Babba DanAgundi ya bayyana cewa, wadanan ‘yan kadan sun ci gaba da aikata laifuka daban-daban na sace-sacen waya da fashi da makami da ma hada baki da masu garkuwa da mutane.


