Kakakin jam’iyyar Peoples Democratic Party PDP, kuma Kwamitin yakin neman zaben shugaban kasa na jam’iyyar PDP a zaben da ya gabata, Daniel Bwala, ya ce, sabuwar dokar takaita bizar da Amurka ta yi wa wasu ‘yan siyasa, shaida ce ta magudin zabe.
Sakataren harkokin wajen Amurka, Antony Blinken, a ranar Litinin din nan ya bayyana cewa gwamnatinsa ta sanya takunkumin hana shige da fice a kan wasu mutane da ake zargi da yi wa dimokradiyya zagon kasa a zaben da aka kammala kwanan nan a Najeriya.
Da yake magana game da lamarin, jigon na PDP wanda ya yi magana a ranar Talata lokacin da ya bayyana a cikin shirin talabijin na Arise, ya yi zargin cewa mutanen da aka sanya hannu kan wannan takunkumin jami’an gwamnati ne.
Karanta Wannan: Amurka ta yi daidai ta hana bisa ga duk wanda ya ci dunduniyar demokradiya – Timi
Ya ce, “Hana ba da takardar izinin shiga Amurka ga wadanda suka yi zagon kasa a zaben ya sake jaddada cewa zaben 2023 ya yi kura-kurai.
“Yawancin wadannan zababbun mutane ne jami’an gwamnati kamar gwamnoni, ministoci, shugabannin ma’aikatun gwamnati da kuma daidaikun mutane masu aiki a madadin gwamnati.”