Wani hamshakin dan kasuwa, Prince Adewole Adebayo, ya zama dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Social Democratic Party (SDP) gabanin babban zabe na 2023.
A zaben da aka shafe sa’o’i da dama ana takun-saka da shi, har zuwa safiyar Alhamis a Abuja, Adebayo ya samu kuri’u 1,546 inda ya doke Khadijah Okunnu-Lamidi wadda ta samu kuri’u 83.
Haka kuma, kuri’u 44 da kwamitin tsare-tsare na babban taron da Cif Segun Oni ya jagoranta ya bayyana rashin sahihancinsa, wanda ya amince da wakilai 1,769 a fadin jihohi 36 da babban birnin tarayya Abuja.
Taron dai ya zo ne a kan sahun daya daga cikin masu neman tsayawa takara, Misis Cesnabmihlo Doroyhy Nuhu-Akenova, wadda ta fice daga takarar domin marawa Adebayo baya a ranar Talata a wani taron manema labarai.