Rundunar sojin Isra’ila ta tabbatar da cewa gawarwakin mutum shida da aka gano a wani rami da ke birnin Rafah na Gaza na mutanen da Hamas ta yi garkuwa da su ne a harin ranar 7 ga watan Oktoba.
Ta bayyana sunayensu tare da cewa cikinsu akwai Ba’amurke wanda ya fito a wani bidiyon Hamas a watannin baya an yanke hannunsa.
Shugaba Biden ya bayyana mutuwarsa a matayin abin takaici, yana mai cewa shugabannin Hamas za su É—anÉ—ana kuÉ—arsu kan abin da suka aikata.
Kungiyar ‘yan’uwan mutanen da ake garkuwa da su sun sake yin kira ga firaminista Benjamin Netanyahu ya amince da yarjejeniyar tsagaita wuta domin sako sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.