fidelitybank

Hamas ta saki Mata uku ƴan Isra’ila

Date:

Hamas ta saki wasu mata uku daga cikin ‘yan Isra’ila da ta yi garkuwa da su tsawon wata goma sha biyar, inda ta danƙa su a hannun ƙungiyar agaji ta duniya ta Red Cross.

‘Yan Isra’ila da dama a birnin Tel Aviv na kasar sun yi ta shewa da murnar sakin nasu da suka kalla a labarai a wani katon allon talabijin da aka girke a birnin. In ji BBC.

Sakin nasu ya kasance ne a wani mataki na aiwatar da yarjejeniyar dakatar da buɗe wuta a tsakanin Hamas da Isra’ila, wadda aka daɗe ana fatan gani.

Matasan matan uku su ne – Doron Steinbrecher, da Romi Gonen da kuma Emily Damari.

Ita ma Hamas ta ce Isra’ila za ta saka mata da sakin aƙalla fursunoni Falasɗinawa 90 a yau, yawanci mata da matasa.

A nan gaba ne kuma Hamas ɗin za ta sake sakin wasu ƙarin ‘yan Isra’ilan talatin amma a rukuni-rukuni a tsawon mako shida.

‘Yan sa’o’i kafin fara aiwatar da yarjejeniyar dakatar da buɗe wutar, hukumar kai ɗauki da Hamas ke tafiyarwa a Gaza ta ce Isra’ila ta kashe aƙalla Falasɗinawa 19 a sababbin hare-hare da ta kai Gaza ta sama.

bbc news 
nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

‘Yan Arewa su dakata da neman mulki har zuwa 2031 – Sakataren Gwamnati

Sakataren gwamnatin tarayya, SGF, George Akume, ya yi kira...

Matatar Dangote ta janye ƙarar da ta shigar kamfanin NNPCL a kotu

Matatar man Dangote ta janye ƙarar da ta shigar...

Ba mu baiwa Obi shawara ya janye daga takara ba – Kungiyar Inyamurai

Kungiyar koli ta al’adun kabilar Igbo, Ohanaeze Ndigbo Worldwide,...

Dole ne APC ta bar mana kujerar mataimakin shugaban kasa – ANPP

Tsagin tsohuwar jam'iyyar All Nigeria Peoples Party wato ANPP...

Gwamna ya nada Sarkin Gusau

Gwamnan jihar Zamfara, Dauda Lawal ya amince da naɗin...

‘Yan Bindiga sun yi ikirarin kashe Daliban koyon aikin lauya a Benuwai

Ƴanbindiga da suka yi garkuwa da ɗaliban makarantar samun...

Tinubu ya gwangwaje tawagar Super Falcons da ruwan daloli da gidaje a Abuja

Shugaban kasa, Bola Tinubu, ya bai wa ƴan wasan...

Super Falcons ta sauka a Abuja tare da yin zagayen nuna kofi

Tawagar Super Falcons ta Najeriya sun isa Abuja bayan...

Za a fuskanci katsewar wutar lantarki a Legas tsawon kwana 25

Masu amfani da wutar lantarki a jihar Legas na...

‘Yan Najeriya ku daina bayar da bayan katin dan kasar ku – NIMC

Hukumar Kula da shaidar ɗan ƙasa (NIMC), ta bayyana...

Likitoci a Legas sun fara yajin aiki saboda rage musu albashi

Ƙungiyar likitoci ta Legas (Medical Guild), wacce ke ƙarƙashin...

Yan Bindiga sun yi wa Mutane 38 yankan Rago a Zamfara

Ƴanbindiga sun kashe wasu mutum 38 ta hanyar yi...
X whatsapp