fidelitybank

Hamas ta saki ƙarin Isra’ilawa uku a Gaza

Date:

Bayan sanya hannu a dakardu tsakanin Hamas da wakiliyar ƙungiyar Red Cross, Hamas ta saki ƙarin mutum uku cikin waɗanda aka tsara za ta saki yau Asabar, ‘yan Isra’ila da ta yi garkuwa da su.

A wannan rukunin na mutum uku mayaƙan ƙungiyar sun fara sakin mutum na farko Eliya Cohen mai shekara 27.

Sai kuma suka saki Omer Shem Tov mai shekara 22 da kuma na uku Omer Wenkert, mai shekara 23, waɗanda Hamas ta kama su a bikin waƙe-waƙe na Nova, ranar 7 ga watan Oktoba na 2023, inda aka danƙa su ga ƙungiyar Red Cross a yau ɗin.

A wannan karon ana miƙa su ne a garin Nuseirat, wanda ke tsakiyar Zirin Gaza.

Bayahude na huɗu da aka tsara Hamas ɗin za ta saki yau shi ne Hisham al-Sayed, wanda ta yi garkuwa da shi tun 2015 bayan da ya tsallaka zuwa Gaza shi kaɗai.

Za kuma a sake shi ne nan gaba a yau ba tare da wani gangamin jama’a ba.

Ana sa ran Isra’ila za ta saki Falasɗainawa sama da 600 daga cikin waɗanda take tsare da su a gidajen yarinta a madadin Yahudawa huɗu da Hamas ke saki yau.

legitnews

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp