Firaministan Isra’ila ya ce, gomman mayaƙan Hamas sun ajiye makamansu tare da miƙa wuya.
Cikin wata sanarwa da aka fitar a jiya Lahadi, Benjamin Netanyahu ya ce “ana ci gaba da yaƙin gadan-gadan” sannan samun galaba a kansu zai ɗauki ɗan lokaci amma ya bayyana cewa “ƙarshen Hamas ya zo”.
A cewarsa, ina faɗa wa mayaƙan Hamas: ta faru ta ƙare. Kar ku sadaukar da ranku ga [Jagoran Hamas Yahya] Sinwar. Ku miƙa wuya – yanzu,” in ji shi.