Ƙungiyar Hamas ta Falasɗinawa, wadda ita da Hezbollah ke samun goyon bayan Iran, ta jajanta wa Hezbollah rasuwar jagoranta, Hassan Nasarallah.
Cikin wata sanarwa da ƙungiyar da ke Gaza ta fitar, ta ce tana alhinin rasuwar shugaban na Hezbollah, sannan ta ce tana tare da ‘yan ƙungiyar Hezbollah da ke Lebanon.
Yayin da aka kwashe tsawon gomman shekaru ana yaƙi tsakanin Isra’ila da Hezbollah, na baya-bayan na ya faru ne bayan harin da Hamas ta ƙaddamar cikin Isra’ila ranar 7 ga watan Oktoban bara, tare da kisan kusan mutum 1,200.
Faɗa tsakanin Hezbollah da Isra’ila ya fara ne a ranar 8 ga watan Oktoban 2023, kwana guda bayan harin na Hamas.
Hezbollah ta riƙa harba rokoki zuwa cikin Isra’ila domin nuna goyon bayanta ga Falasɗinawa, kuma ta alƙawarta ci gaba da hakan, har sai an cimma yarjejeniyar tsagaita wuta a yaƙin Gaza.


