Jiniyar da ke alamta kai hari ta yi kuka a tsakiyar Isra’ila bayan Hamas ta kaddamar da hare-haren roka kan birnin Tel Aviv cikin mintuna kalilan da suka wuce.
Hukumomin ba da agajin gaggawa na Isra’ila sun ce ba a samu rahoton wanda ya ko jikkata ba zuwa lokacin kawo wannan rahoto daga birni na biyu mafi girma a Isra’ila da kuma wasu wuraren, sai dai wasu da suka ji raunuka a lokacin da suke kokarin neman mafaka


