An ji karar fashewar rokoki da dama, daidai lokacin da wa’adin da kungiyar Hamas ta bayar na karfe 5 na yamma agogon yankin, cewa mazauna birnin Ashkelon su fice, ya cika.
Wakiliyar BBC Alice Cuddy daga birnin Ashkelon ta ce suna tare da wasu mazauna birnin a gidan da suke fakewa.
Dukkansu, a cewarta suna duba wayoyin salula tare da jira cikin zakuwa don ganin abin da zai faru a gaba.
Ta ce sun ji karin fashewar abubuwa a cikin ‘yan mintunan da suka wuce.