fidelitybank

Halin Tsaro: Gwamna ya dakatar da Basarake mai daraja ta ɗaya a Kogi

Date:

Gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayar da umarnin dakatar da wani basarake mai daraja ta daya, Ohi na Eganyi wanda ke rike da mukamin shugaban majalisar gargajiya ta Ajaokuta, Alhaji Musa Isah Achuja, ba tare da bata lokaci ba.

Gwamnan, a wata wasika da ya aikewa kwamishinan kananan hukumomi da masarautu na jihar, ya umurci shugaban karamar hukumar Ajaokuta, Mustapha Aka’aba, da a tambayi shugaban karamar hukumar Ajaokuta, kan tabarbarewar tsaro a Ajaokuta tare da umartar shugaban da ya amsa cikin Sa’a 24.

Umarnin gwamnan ya biyo bayan tabarbarewar tsaro a yankin na baya-bayan nan wanda ya yi sanadin mutuwar wasu jami’an tsaro, bisa halalcinsu na tabbatar da doka da oda.

Gwamnan ya yi kakkausar gargadi ga sauran sarakunan gargajiya a fadin jihar da ka iya alakanta su ta wata hanya ko kuma wata alaka da masu aikata miyagun laifuka a yankunansu da su kau da kai.

A cewarsa, gwamnatinsa za ta yanke mu’amala da duk wanda ke soyayya da masu aikata laifuka komai girmansa.

Gwamna Yahaya Bello, a wata sanarwa a ranar, 31 ga watan Yuli, ta hannun babban sakataren yada labaran sa, Onogwu Muhammed, ya kuma umurci duk wani yunkuri na shugabannin kananan hukumomin na fita daga yankunansu da sauran tafiye-tafiye ba tare da bin ka’ida ba.

Gwamnan ya yi gargadin cewa, babu wata alaka da masu aikata miyagun laifuka da za su hana shi daga babban nauyin da ke kansa na kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa da mazauna jihar.

sun news paper

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp