fidelitybank

Hakar Ma’adanai: An tsamo gawarwaki a kalla mutane 32 a Sudan

Date:

Masu aikin ceto na ci gaba da kokarin curo wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata daga wata mahakar zinare a wani yanki mai nisa a kasar Sudan.

Lamarin ya faru ne tun a ranar lahadi, inda akalla mutane 32 su ka mutu a cikin ramin da ya rufta dasu.

Ya zuwa safiyar Larabar, an gano gawarwaki 32 daga mahakar ma’adinan a yammacin Kordofan baya ga wasu mutane uku da aka ceto sun jikkata, kamar yadda, Khaled Dahweya, daraktan kamfanin albarkatun ma’adinai na Sudan mallakin gwamnatin jihar a yammacin Darfur ya sanar da hakan a ranar Laraba.

Mahakar ma’adinan ta rufta ne da yammacin Lahadin da ta gabata, yayin da, kimanin mutane 40 ne ake kyautata zaton na cikin ramin mai zurfin sama da mita 20 (kafa 65).

Ya kara da cewa, hatsarin ya afku ne a yankin da ake yawan hako ma’adinai ba tare da la’akari da ka’idojin tsaro ba.

Zinariya ita ce kayayyaki mafi daraja a kasar Sudan wanda ake kai su zuwa ketare, amma yawancin karafan ana siyar da su a wajen tashoshi na hukuma, galibi ana siyarwa a Dubai.

Kasar Sudan dai ta sha fama da matsalar tattalin arziki da ta dade tana fama da shi, wasu kuma sun koma aikin hako ma’adinai a yankunan da ba su ci gaba ba, domin kokarin samun rayuwa.

punch newspaper nigeria

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp