fidelitybank

Haka kurin laifin wani ya shafe ni ban amince ba – Shugaban EFCC

Date:

Shugaban hukumar yaki da yi wa tattalin arzikin kasa ta’annati EFCC, AbdulRasheed Bawa ya ce, ya daukaka kara dangane da hukuncin da wata kotun birnin tarayya ta yanke masa ranar Talata a Abuja.

Kotun yanke hukuncin tura shi gidan yari sakamakon kama shi da laifin raina umarnin kotu.

Tun da farko dai kotun ta umarci shugaban da ya mayar da wasu kudi da suka kai naira miliyan 40 da wata motar alfama da hukumar ta karba daga wani mutum da ta zarga da laifin rashawa.

Shugaban EFCC, ya ce, shi a karan kansa bai yi watsi da umarnin kotun ba a matsayinsa na shugaban hukumar, ballantana ya fuskanci fushin kotu, saboda a saninsa kotun ta bayar da umarnin ne tun a ranar 21 ga watan Nuwamban 2018.

Wato shekara uku kenan kafin ya zama shugaban hukumar ta EFCC, dan haka ba shi aka bai wa umarnin ba kuma a cewarsa babu yadda za a yi laifin wani ya shafe,

Ya kara da cewa ”Mun riga mun daukaka kara game da wannan hukunci, dan haka za mu jira domin ganin yadda shari’ar za ta kasance”

Amma ya ce duk da haka ya bayar da umarni a mayar da wannan motar alfarma ga mai ita tun a ranar 27 ga watan Yunin wannan shekarar, tare da bayar da umarnin bin hanyar da ta dace wajen mayar da kudin naira miliyan 40 ga mai su.

www.nigeriannewspapers.com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp