Wata Hajiya daga jihar Jigawa, Hajiya Rabi Mohammed Mohammed, ta rasu a kasar Saudiyya.
Jami’in shiyyar Malam Madori a Jihar Jigawa Alhaji Abdullahi Adamu Tahir ya tabbatar wa manema labarai hakan a birnin Makkah na kasar Saudiyya.
Ya ce marigayin ya rasu ne a Asibitin Sarki Abdulaziz da ke Makkah a daren Juma’a bayan gajeriyar rashin lafiya.
A cewarsa, marigayin dan karamar hukumar Malam Madori ne.
Jami’in shiyyar, Tahir, ya ce an sanar da iyalan marigayi alhazan.
Darakta Janar na Hukumar Alhazai ta Jihar Alhaji Ahmed Umar Labbo ya jajantawa iyalan mamacin.
Hukumar ta yi addu’ar Allah SWT ya jikan mamacin, ya gafarta mata zunubanta, ya ba ta matsayi mafi girma a gidan Aljannah, ya kuma jajantawa iyalanta bisa wannan rashi mara misaltuwa.
Za’ayi Sallar Jana’iza ta Marigayi Hajiya Rabi’u Mohammed bayan Sallar Magrib a Masallacin Harami na Makkah, yau Asabar 29 ga watan Yuni 2024.