Manyan hafsoshin tsaro na kungiyar ECOWAS a yammacin Afirka, za su yi taro a yau Laraba a Abuja, Najeriya, domin tattaunawa kan juyin mulkin da aka yi a jamhuriyar Nijar, a cikin wata sanarwa da kungiyar ta fitar a ranar Talata, NAN ta ruwaito.
Ku tuna cewa a ranar Lahadin da ta gabata ne shugabannin kungiyar tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka suka sanyawa Nijar takunkumi tare da gargadin cewa za su yi amfani da karfin tuwo a kan mulkin soja.
Sun bai wa gwamnatin mulkin soji mako guda ta dawo da shugaba Bazoum, wanda ake tsare da shi.
Tun da farko, gwamnatin mulkin sojan ta yi gargadin cewa za ta bijirewa duk wani “shirin cin zarafi ga Nijar” daga kasashen yammacin duniya ko na yankin.
Sanarwar da aka fitar bayan taron kolin na ranar Lahadi a Najeriya ta ce kungiyar ECOWAS ba ta da hurumin juyin mulki.
Kungiyar kasashen yankin ta ce za ta dauki dukkan matakan da suka dace don maido da tsarin mulkin kasar idan ba a biya bukatunta cikin kwanaki bakwai ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Irin wadannan matakan na iya hada da amfani da karfi,” kuma shugabannin sojoji za su gana “nan da nan” don shirya shiga tsakani.