Erling Haaland ya zama gwarzon dan wasan Uefa na kakar 2022/23.
Haaland ya taimaka wa kungiyarsa lashe kofuna uku a kakar wasa da ta wuce, inda ya zura kwallaye 52.
Aitana Bonmati ‘yar wasan Sifaniya ce ta zama gwarzuwar ‘yar wasa tsakanin takwarorinta mata.
Sarina Wiegman kociyar tawagar mata ta IUngila ce ta lashe kyauta bayan jagorantar tawagar zuwa wasan karshe na gasar cin Kofin Duniya ta Mata, sannan ta dauki kofin Finalissima bayan doke Brazil a filin wasa na Wembley.
Pep Guardiola na Manchester City ne ya lashe kyautar gwarzon kocin maza mafi ƙwazo na Uefa na kakar wasa ta 2022/23.
Kocin na Manchester City ya taimaka wa kungiyarsa lashe kofuna uku a kakar wasa da ta wuce..


