Gwamna Bello Matawalle ya yi kira ga shugabanni da magoya bayan jam’iyyar All Progressives Congress (APC) da su gyara gidansu, domin jam’iyyar ta ci gaba da mulki a 2023.
Matawalle ya yi wannan kiran ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a ranar Litinin a filin jirgin saman Sultan Abubakar, Sokoto wanda zai tafi Gusau, babban birnin jihar Zamfara.
Ya danganta nasarar sulhun da aka samu tsakanin masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a jihar da sa hannun Allah.
“Ba ni na yi ba, amma Allah ne ya sa baki. Yanzu da muka zama daya da iyali daya a jihar Zamfara, za mu hada kai mu mayar da hankali kan zaben 2023 tare da tabbatar da cewa, jam’iyyarmu ta samu nasara a dukkan matakai.
“Da wannan sulhu, ina da yakinin cewa, APC za ta lashe dukkan zabuka a zaben 2023,” in ji gwamnan.
Kamfanin Dillancin Labaran na Ƙasa NAN, ya bayar da rahoton cewa, a ranar 9 ga watan Mayu, Sanata Abdullahi Adamu shugaban jam’iyyar APC na kasa ya sanar da warware rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar a Zamfara.