Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya ce, gwamnati ta fara rabon kayan abinci da kayan sawa na sama da Naira biliyan 1.8 ga talakawa a fadin jihar.
Matawalle ya kaddamar da rabon kayan ne a ranar Asabar da ta gabata, domin ganin an fara azumin watan Ramadan a garin Gusau.
Gwamnan ya ce, kayayyakin sun hada da buhunan abinci 125,701 da kayan sawa guda 40,000. A cewar The Nation.
“Yayin da muke bikin ranar daya ga wata mai alfarma, na yi matukar farin ciki da kaddamar da rabon kayan abinci na watan Ramadan ga al’ummar Zamfara duk shekara. Mun sayo kayayyakin na ciyarwa da jin dadin watan Ramadan akan jimillar Naira 1,818,209,000.