fidelitybank

Gwanar da ta shafe kwanaki 10 ta na girki ba kakkautawa

Date:

Gwanar girkin ƙasar Ghana Failatu Abdul-Razak ga alama ta karya tarihin duniya, bayan ta kwashe tsawon fiye da sa’a 227 tana zuba girki babu ƙaƙƙautawa.

Lulluɓe da tutar ƙasar, Failatu Abdul-Razak ta kawo ƙarshen girkin tsawon kwana goma, cikin jinjina da yabo daga cincirindon mutane a ranar Laraba.

Gabanin ta fara girkin nata, ta bayyana fafutukar da ta sanya gaba a matsayin “aikin ƙasa”, inda ta ce tana yi ne domin Ghana.

Mutane sun yi ta sowa lokacin da ta fito daga ɗakin girke-girke na otel ɗin da ta yi bajintar a birnin Tamale.

Jami’an da ta yi aiki da su, sun ce za ta aika shaidar aikinta ga kundin bajinta na duniya Guinness World Records don tabbatarwa bisa ƙa’ida cewa ta karya tarihin da aka taɓa kafawa a baya.

Mai riƙe da kambin tarihin na yanzu ɗan ƙasar Ireland Alan Fisher, ya yi girki tsawon sa’a 113 da minti 57.

Gwanar girkin ta Ghana ta ce tana so ne ta tabbatar cewa duk wanda ya yi ƙoƙarin karya tarihinta, sai ya sha matuƙar “wahala”.

‘Yan siyasa, ciki har da mataimakin shugaban ƙasa Mahamudu Bawumia, da ɗumbin fitattun mutane kai har da rundunar sojojin Ghana sun bayyana goyon bayansu ga gwanar girkin a tsawon lokacin da ta ɗora sanwa.

tribune news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp