Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaha, ya sa hannu kan ƙudurin dokar kula da masu buƙata ta musamman, wadda ta ƙunshi kafa hukumar masu buƙata ta musamman.
An yi dokar ce domin samar da daidaito da adalci, tare da tsara hanyoyin da za a taimakawa mutane masu buƙata ta musamman a jihar da kuma tabbatar da cewa ana damawa da su.
A lokacin bikin sa hannu kan dokar a gidan gwamnatin, Gwamna Inuwa ya sanar da naɗa Ishiyaku Adamu a matsayin shugaban sabuwar hukumar kula da masu buƙata ta musamman da ya kafa.
Ya ce tun da ya hau kujerar gwamna yake ƙoƙarin kula da masu buƙata ta musamman, inda a cewarsa hakan ya sa ya tun a farko ya naɗa mai taimaka masa na musamman kan harkokinsu.
Shugaban sabuwar hukumar, Ishiyaku Adamu, ya yi godiya ga gwamnan, tare da yaba masa bisa cika musu alƙawarin da ya yi.