Gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, ya ayyana ranar Litinin 1 ga watan Agusta, 2022, a matsayin ranar da babu aiki, domin murnar shiga sabuwar shekarar Musulunci ta 1445.
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yada labarai, Malam Muhammad Garba ya raba wa manema labarai a Kano.
Gwamnan ya taya daukacin al’ummar musulmi murnar shiga sabuwar kalandar Musulunci.
Sai dai ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da hutun da aka basu dasu yi addu’ar neman gafarar Allah da kuma sa baki wajen ceto kasar nan daga matsalolin tsaro da ke addabar kasar.
Gwamna Ganduje ya kuma bada tabbacin shirin gwamnatin sa na cigaba da inganta rayuwar al’ummarta.