Ƙungiyar gwamnonin kudancin Najeriya ta Southern Governors Forum (SGF) ta yaba wa takwarorinsu na arewaci musamman Badaru Abubakar na Jihar Jigawa game da janyewa daga neman takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar APC da ya yi.
Wata sanarwa da shugaban SGF kuma Gwamnan Jihar Ondo Rotimi Akeredolu ya sanya wa hannu ta ce “da ma abin da muke tsammani ke nan daga ‘yan uwanmu masu kishin ƙasa”.
Sanarwar ta nemi sauran ‘yan takara daga Arewa da su yi koyi da Gwamna Badaru wajen janyewa su ƙyale ‘yan Kudu su fafata a akwatin zaɓe.
“Muna taya ɗan uwanmu Gwamna Badaru murna game da halin kirki da ya nuna,” a cewar sanarwar. “Har abada za a dinga yaba masa.”
Sai dai Badaru ya faɗa wa BBC Hausa cewa yana jiran Shugaba Buhari ya amince da janyewar tasa tukunna.
Bayan ganawarsu da shugaban ƙasa, su ma gwamnonin kudancin Najeriya ƙarƙashin jagorancin Akeredolu suka yi wata ganawa a Abuja babban birnin ƙasar ranar Asabar da dare.