fidelitybank

Gwamnonin G5 sun gindaya sharuda na yin sulhu da Atiku

Date:

Da alamu dai rikicin da ya dabaibaye jam’iyyar PDP ya zo karshe bayan da shugabannin jam’iyyar suka cimma matsaya da gwamnonin PDP na G5.

Mambobin Gwamnonin PDP G5, karkashin jagorancin Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, sun yi takun-saka da Atiku, bayan da Wike ya kasa lashe tikitin takarar shugaban kasa na jam’iyyar.

Sauran mambobin G5 sun hada da: Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo, Samuel Ortom na jihar Benue, Okezie Ikpeazu na jihar Abia, da Ifeanyi Ugwuanyi na jihar Enugu.

Haka kuma G5 din ba su ji dadin yadda Atiku ya ki amincewa da Wike a matsayin mataimakinsa ba tare da neman Iyorchia Ayu ya sauka daga mukaminsa na Shugaban jam’iyyar, bisa zarginsa da rage karfin jam’iyyar PDP daga Arewa.

Sai dai kuma alamu sun nuna cewa da alama tsohon shugaban kasa na mulkin soja, Janar Ibrahim Badamasi Babangida (rtd) ne ya kawo karshen rikicin da ya dabaibaye babbar jam’iyyar adawa.

Wani jigon jam’iyyar, wanda ya gwammace a sakaya sunansa, ya ce, G5 sun amince su yi wa dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar, Atiku Abubakar aiki, idan har za a biya musu sabbin bukatunsu.

Bukatun nasu, a cewar majiya mai tushe, ita ce: “Ya kamata a raba manyan ma’aikatun gwamnati tsakanin shiyyoyin siyasa guda shida;

“Ya kamata a raba manyan jami’an tsaro a dukkan shiyyar siyasa da kuma cewa dukkan ofisoshin jam’iyyar a Kudu su koma Arewa idan Atiku ya yi nasara.”

legits news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Iran ta dakatar da tashin jirgi a Ĉ™asarta

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Iran ta...

Poland za ta kwashe dukkannin Ĉ´an Ĉ™asarta daga Isra’ila

Poland na shirin kwashe kusan ‘yan kasarta 200 daga...

Kisan Binuwai abun haushi ne bai kamata a Ĉ™yale ba – Atiku

Atiku Abubakar ya yi Allah-wadai da Kisan Benue, tare...

Ĉ³an Bindiga sun ajiye makamai a Katsina

Wasu fitattun jagororin Ĉ´anbindiga da suka addabi yankunan Ĉ™aramar...

Iran ta rataye Mutumin da ya yi mata leĈ™en asiri

Iran ta ce ta aiwatar da hukuncin kisa ga...

Isra’ila ta ci gaba da neman Mutanen da suka maĈ™ale

Tawagar masu aikin ceto a Isra'ila na ci gaba...

Kotu ta bayar da umarni a kashe Matashi ɗan shekara 23 a Kano

Babbar kotun jihar Kano mai lamba 23 Ĉ™arĈ™ashin mai...

Iran ta na ci gaba da luguden makami a kan Isra’ila

Iran ta ci gaba da lugudan wuta a Isra'ila...

An yi sulhu da shugabannin Ĉ´an Bindiga a Katsina

Wasu al'ummar Katsina, sun yi sulhu da wasu shugabannin...

Za a fuskanci ambaliya a wasu jihohin – NIMET

Hukumar kula da yanayi ta NiMet, ta ce akwai...

Za mu mayar wa da Isra’ila martani mai tsanani – Iran

Shugaban Ĉ™asar Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi alwashin mayar...

Ba za mu taɓa barin Iran ta Ĉ™era makamai masu linzami ba – Isra’ila

Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce burin Ĉ™asarsa shi...
X whatsapp