Rundunar ‘yan sanda ta gargaÉ—i wasu gwamoni da take zargi na daukar nauyin ‘yandaba domin ingiza rikici.
Babban sufeta janar na ‘yan sanda, Usman Baba, ya ce, suna samun rahotanni sosai daga jihohi kan yadda wasu gwamnoni ke karfafa dabanci tsakanin matasa da kai wa ‘yan hamayya hari.
Usman Baba, ya ce, za su dau mataki mai tsauri domin daƙile duk wani yunkuri yada kiyayya ko haddasa rikici bisa tanadin dokokin kasar.
Jami’in ya kuma umarci ‘yan takara musamman masu neman kujerar shugaban kasa su mutunta yarjejeniyar da suka sanyawa hannu na tabbatar da zaman lafiya kafin zabe da lokacin zabe da kuma bayan zabe.