Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta yi kira da a kwantar da hankali bayan kisan wata matashiya da aka zarga da yi wa Manzon Allah ɓatanci a Jihar Sokoto.
A sanarwar da kafofin yaɗa labarai suka ruwaito, gwamnan Filato kuma shugban ƙungiyar Simon Lalong ya ce ƙungiyar tasu na cikin damuwa game da halin da ake ciki a Sokoto.
“Gwamnonin sun damu da abin da ke faruwa, wanda lamari ne da ya saɓa wa sashen shari’a wajen ɗaukar mataki,” a cewar Lalong.
“Gwamnonin Arewa na kiran a zauna lafiya bayan rahotannin rikiɗewar zanga-zangar lumana zuwa rikicin da ya sa aka saka dokar hana fita a birnin Sokoto.”
Kazalika, gwamnonin sun ce duk wani yunƙuri na ɗaukar doka a hannu, kan lamarin addini ko akasin haka – “zai iya tayar da ƙarin rikici”.