fidelitybank

Gwamnonin APC sun ki amincewa da wa’adin CBN

Date:

Gwamnonin jihohi da aka zaba a karkashin jam’iyya mai mulkin kasar ta APC, sun ki amicewa da wa’adin 10 ga watan Fabrairu da babban bankin Najeriya ya shata wa al’ummar kasar na su kamala sauya tsofaffin takardun naira na N1000, N500 and N200 da sababbin da ya fitar.

Gwamnonin sun ce bayanan da ke isa garesu daga al’umominsu sun tabbatar musu cewa al’umomin na shan bakar wahala cikin ‘yan kwanakin da suka gabata yayin da suke kokarin sauya takardun kudin, saboda lokacin da bankin ya bayar bai zo a lokacin da ya dace ba da kuma dalilin illar da matakin ke yi wa tattalin arzikin kasar.

Wannan ne yasa suka yanke shawarar ganawa da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da misalin karfe 10 na safiyar Juma’a.

Karanta Wannan: Da Dumi Dumi: CBN ya umarci Bankuna su fara biyan sababbin kudi

Cikin jihohi 36 na Najeriya, jam’iyyar APC na iko da jihohi 21 ne.

Gabanin yanke wannan hukuncin ganawa, gwamnonin sun zabi gwamna Babajide Sanwo-Olu (Lagos) da Nasir El-Rufai (Kaduna) da Mai Mala Buni (Yobe) da kuma Dapo Abiodun (Ogun) domin su gana da gwamnan babban bankin Godwin Emefiele, kuma yayin tattaunawar da suka yi, sun sanar da shi rashin gamsuwarsu da “garaje da hanzarin” da ake nunawa na aiwatar da sauyin takardun kudin.

Sun kuma sanar da Mista Emefiele cewa babban bankin Najeriya ya gaza a aikin da aka ba shi na sauya takardun kudin ganin yadda ‘yan Najeriya ke fafutukar karbar takardun kudinsu da suka ajiye da kawunansu a bankunan kasar.

breaking news in nigeria today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp