Gwamnonin Jam’iyyar APC, sun yi ganawar sirri da maraicen ranar Laraba, domin tattauna al’amuran da suka shafi jam’iyyar, bayan saukar shugaba da sakataren jam’iyyar Sanata Abdullahi Adamu da Sanata Iyiola Omisore.
Saukar mutanen biyu, ya sanya nan take jam’iyyar ta sanar da naÉ—in mataimakain shugaban jam’iyyar na yankin arewaci, Sanata Abba Kyari a matsayin shugaban riÆ™o na jam’iyyar.
Taron gwamnonin, ƙarƙashin jagorancin shugaban ƙungiyar gwamnonin APC Sanata Hope Uzodinma, ya samu halartar gwamnonin jihohin Ekiti da Ebonyi da Niger da Benue da Kaduna da Legas da Yobe da Katsina da Kebbi da muƙaddashin gwamnan jihar Ondo, kamar yadda Gidan Talbijin na Channels TV ya ruwaito.
A ranar litinin ne dai kwamitin gudanarawar jam’iyyar ya tabbatar da nadin Sanata Kyari a matsayin shugaban riÆ™o na jam’iyyar.
A shekarar da ta gabata ne aka zaÉ“i Sanata Abdullahi Adamu a matsayin shugaban jam’iyyar, a babban taron da jam’iyyar ta gudanar a Abuja.