Kungiyar Kwadago NLC ta samu tabbaci daga gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje cewa, kungiyar gwamnonin Najeriya za sua yi duk mai yiwuwa wajen ganin an sasanta rikicin da ke tsakanin gwamnatin tarayya da kungiyar malaman jami’o’i (ASUU).
Ya yi alkawarin ne ga mambobin kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar da ke gidan gwamnati suna gudanar da zanga-zangar nuna goyon baya ga ASUU, a ranar Talata.
Gwamnan ya bayyana nadamar rikicin da aka dade yana kuma yi alkawarin cewa kungiyar ta NGF za ta yi tasiri ga gwamnatin tarayya a fannin shawarwari a kokarin kawo karshen lamarin tare da hana tsarin gaba daya rugujewa.
“Za mu yi galaba a kan Gwamnatin Tarayya ta fannin shawarwari domin dole ne a magance rikicin domin a ceto tsarin.
“Dole ne a warware wannan rikicin don taimakawa wajen ceto tsarin. Ba ma son rugujewar tsari a kasar nan ko kadan,” in ji Ganduje.
Ya ci gaba da cewa, “Ni da takwarorina daga dukkan jihohin kasar nan 36, ba tare da la’akari da bambance-bambancen jam’iyyarmu ba, mun damu da daukar matakin yajin aikin da aka tsawaita, kuma za mu hada kawunanmu domin kawo karshen rikicin.
Masu zanga-zangar da suka hada da dalibai da kuma ’yan kungiyar kwadago, gwamnan ya yaba da irin balaga da suka nuna wajen ganin an gudanar da muzaharar cikin lumana.