Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Inuwa Yahaya, ya bayyana kaɗuwarsa kan mutuwar dattijo tsohon ministan noma, Audu Ogbeh – wanda ya rasu ranar Asabar 9 ga Agustan 2025, yana da shekara 78.
“A madadina da sauran gwamnonin arewa muna miƙa ta’aziyya kan rasuwar wannan dattijo, mai faɗa a ji wanda ya sadaukar da rayuwarsa wajen cigaban ƙasa,” in ji Inuwa Yahaya a cikin wata sanarwa.
Ya ce Ogbeh jagora ne na gari kuma ƙwararren ɗan siyasa wanda za a ci gaba da tunawa da irin rawar da ya taka wajen cigaban dimokraɗiyya a Nijeriya.
“Ya kawo mutunci da sanin ya kamata a kowane mukami da ya riƙe, ya kuma bautawa ƙasarsa da nagarta.
Shugaban gwamnonin arewar ya ce mutuwarsa ba rashi ne ga jihar Benue kaɗai ba, har ma da Najeriya baki ɗaya.