Gwamnonin arewa maso yamma sun gudanar da taro kan inganta tsaro wanda ya gudana a Katsina.
Hukumar raya ƙasashe ta Majalisar Dinkin Duniya ke shirya taron wanda ake fatan fito da hanyoyin da za a kawo karshen matsalar tsaro a yankin.
Cikin masu halartar taron har da mataimakin shugaban kasa Khashim Shatima da manyan jami’an tsaro da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Taron na kwana biyu na da nufin inganta tsaro a yankin arewa maso yammacin kasar nan kuma zai mayar da hankali ne, wajen samun hadin gwiwar gwamnatocin yankin domin tsare rayukan al’umma da sana’o’in su.