Gwamnatin tarayya ta ce, za ta daina ciyar da fursunonin jihohi da ke tsare a gidajen yarin ƙasar daga ƙarshen wannan shekara.
Ta shawarci jihohin ƙasar su yi cikakken amfani da gyaran fuskar da aka yi wa tsarin mulkin Najeriya a baya-bayan nan, don kyautata rayuwar fursunoninsu.
Wata sanarwa daga ma’aikatar cikin gida, ta ambato Ministan cikin gida, Rauf Aregbesola na cewa matakin, zai fara aiki ne daga ranar 31 ga watan Disamban 2023.
Ya yi shelar cewa Shugaba Muhammadu Buhari ya sa hannu a kan dokar yi wa tsarin mulkin Najeriya gyaran fuska, abin da ya cire harkar kula da gidajen yari daga ƙarƙashin ikon gwamnatin tarayya kaɗai, zuwa ƙarƙashin ikon haɗin gwiwar gwamnatin tarayya da jihohi.
Don haka in ji sanarwar ma’aikatar cikin gida “Daga ranar 1 ga watan Janairun 2024, gwamnatin tarayya za ta daina ciyar da ɗaurarrun da suka aikata laifuka a jihohi amma ake tsare da su a gidajen yarin tarayya.
Jazaman ne kuma, jihohi su fara yin kasafin kuɗi don ciyar da ɗaurarrunsu da ke gidajen yarin tarayya a daidai lokacin da muke jiran su gina gidajen yari na kansu.”
Ya ce matakin zai taimaka wajen ƙara rage cunkoso a gidajen yarin Najeriya.
Ministan ya ce mutanen da suka aikata laifi a jihohi ne fiye da kashi 90% na ɗaurarrun da ke gidajen yarin Najeriya a yanzu.