Shugaba Muhammadu Buhari, ya ce, gwamanonin jihohin kasar nan na sace kason kudaden da ake tura wa kananan hukumomi duk wata daga asusun tarayya.
Shugaban ya yi wannan zargi ne a taron manyan jami’an gwamnati na wannan shekara, na cibiyar nazarin manufofi da dabaru ta kasa (NIPSS) da ke Kuru, a Jos.
A duk shekara dai masu yin kwas a cibiyar, sukan dauki wani muhimmin lamari da ya shafi kasa baki daya, su yi nazari game da shi, kuma a karshe su gabatar da sakamakon bincikensu da shawarwarinsu.
A bana sun duba batun mulkin kananan hukumomi ne bayan da Shugaban ya ba su umurnin gudanar da nazari a kan yadda ake gudanar da mulkin kananan hukumomi.
Mai magana da yawun shugaban kasar, Mallam Garba Shehu ya shaida wa BBC cewa manyan jami’an gwamnatin sun kammala aikin nasu kuma sun bayar da shawarwari:
“ Muhimmai a ciki sun hada da rashin tsari na dimukraddiya”
Shugaba Buhari ya ce a yanzu haka jihohi 20 ne kawai suke da zababbun shugabannin kananan hukumomi da jama’a suka zaba.
Ya ce wasu mulki ake yi a karkashin kantoma wanda ba zababbe ba ne kamar yadda Garba Shehu ya bayyana.
”Wuraren da aka zabi shugabannin kananan hukumomi ba lallai ne a ce an rungumi al’umma na kananan hukumomin ana tafiya da su ba.” Kamar yaddaya ce.
”Akwai rashawa da cin hanci, akwai kuma rashin fahimtar aiki, akwai rashin kwarewa na ma’aikata, akwai rashin kudi da za a yi aiki da shi” in ji shi.