Shugaba Bola Tinubu, ya buƙaci gwamnonin ƙasar nan su fifita walwalar ƴan Najeriya ta hanyar zuba jari a ƙauyuka da yankunan karkara, ta hanyar bunƙasa wutar lantarki da ayyukan noma domin kawar da talauci.
Kiran na zuwa ne bayan gabatar da wani shirin gwamnati na musamman kan bunƙasa tattalin arziki a matakin mazaɓu da aka yi wa laƙabi da ‘Renewed Hope Ward Development Programme (RHWDP)’ da ministan kasafi da tsare-tsare na ƙasar ya yi a lokacin taron majalisar tattalin arzikin ƙasar.
Manufar sabon shirin na RHWDP shi ne tabbatar da bunƙasar tattalin arziki ta hanyar taimaka wa mazaɓun ƙasar 8,809 a faɗin jihohin ƙasar 36, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban ƙasar ta bayyana.
Shugaba Tinubu ya kuma buƙaci gwamnonin ƙasar su yi duk mai yiwuwa wajen tallafa wa rayukan ƴan ƙasar daga tushe.
”Ina kira a gare ku, mu ƙara ƙaimi wajen sauya halin da mutanenmu ke ciki a yankunan karkara”, in ji Tinubu, kamar yadda sanarwar ta ambato.
“Tsare-tsaren tattalin arzikinmu na tafiya yadda ya kamata. Mun kama hanyar farfaɗowa, amma muna buƙatar ƙara ƙaimi a yankunan karkara. Mun san halin da ƙauyukanmu ke ciki, don haka mu haɗa hannu wajen yin abin da zai tallafa musu,” in ji shi.