Wakilin mazabar Abia ta Arewa a majalisar dattawa kuma tsohon gwamnan jihar Abia, Sanata Orji Uzor Kalu, ya yabawa hukuncin da kotun koli ta yanke na baiwa kananan hukumomi cin gashin kansu na kudi.
A hukuncin da ta yanke wanda mai shari’a Emmanuel Agim ya karanta, kotun kolin ta umurci gwamnatin tarayya da ta fara biyan kudaden kananan hukumomi kai tsaye zuwa asusunsu na kebantattu.
Kotun kolin ta soki yadda gwamnatocin jahohin kasar suka ki amincewa da bai wa kananan hukumomi cin gashin kansu na harkokin kudi.
Da yake mayar da martani kan hukuncin a cikin wata sanarwa a ranar Juma’a, Kalu, mai wakiltar mazabar Abia ta Arewa, ya yaba wa bangaren shari’a, yana mai bayyana hukuncin a matsayin jajirtacce.
“Hukuncin da kotun koli ta yanke kan cin gashin kan kananan hukumomi abu ne da ya kamata a yaba tare da jinjina masa, musamman saboda jajircewa da ‘yancin kai da bangaren shari’a ya nuna.
“Kotun Koli, kasancewarta kotun siyasa, ta yi abin da ya dace kuma mai amfani ga al’umma. Duk da cewa ana iya yin katsalandan a jihohi, amma mu yarda cewa duk kiraye-kirayen a kawo karshen rashin tsaro, garkuwa da mutane, da ‘yan fashi sun fara ne da wannan ‘yancin cin gashin kai da aka baiwa kananan hukumomi.
“Lokacin da kananan hukumomi ke da ikon sarrafa kudadensu gaba daya, ana samun kwararar kayayyaki da ayyuka a kananan hukumomin. Misali, lokacin da nake gwamna a tsakanin 1999-2007, cin gashin kan shugabannin kananan hukumomi na shi ne babban ci gaba na nasarar gwamnatina.
“Shugabannin kananan hukumomin sun gina tituna sun ba ‘yan kwangilar cikin gida kwangila. Shuwagabannin sun sami damar daukar cikakken alhakin abin da ya faru a karamar hukumarsu, kuma an rage yawan laifuka zuwa mafi karanci.
“Zan kuma yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta duba batun shigar da karar zaben kananan hukumomi da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gudanar a maimakon Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Jiha (SIEC).
“Hakan zai kara karfafa ‘yancin cin gashin kan kananan hukumomi tare da rage matsin lamba ga gwamnatocin jihohi. Lokacin da mulki ya kai ga tudun mun tsira, zai zama da sauki a gane da kuma dora shugabanni alhakinsu.
“Ina kira da gaske ga gwamnonin jihohi 36 da su amince da wannan hukunci a matsayin nasara ga dimokuradiyya, nasara ce ga kansu, kuma nasara ce ga dukkan ‘yan Najeriya,” in ji shi.


