Gwamnatin Jigawa ta fito da sabon tsarin biyan iyaye mata masu juna biyu kudin aljihu duba biyar a duk wata.
Mataimakain Gwamanan Jihar, Mallam Umar Namadi, ya bayyana hakan ne yayin wata ganawa da manema labarai a Dutse, babban birnin Jihar,
Ya ce, jihar ta bullo da shirin ne, domin ta taimaka wa mazauna karkara, saboda su rinka zuwa awon ciki a asibiti kafin haihuwa.
Mataimakin Gwamnan jihar, ya ce, za a fara biyan kudin ne ga mata 5000, daga karshen watan nan na Febrairu.