fidelitybank

Gwamnatin Zamfara ta rufe kafofin yada labarai 6

Date:

Gwamnatin Jihar Zamfara ta ba da umarnin rufe kafofin yaɗa labarai shida saboda zargin saɓa dokokin da gwamnatin ta kafa.

Kwamashinan Yaɗa Labarai Ibrahim Dosara ya faɗa wa BBC Hausa cewa an rufe su ne saboda sun yaɗa taron jam’iyyar adawa ta PDP duk da cewa gwamnatin jihar ta hana tarukan siyasa saboda dalilai na tsaro.

Ya ce Majalisar Tsaro ta Zamfara ce ta amince tare da ba da umarnin rufe gidajen labaran da suka ƙunshi Radio Najeriya, da Pride FM Gusau, da NTA Gusau, da Gamji Talabijin, da Vision FM, da Al Umma TV.

Sai dai jam’iyyar PDP a jihar ta musanta zargin karya dokar, tana mai cewa hukumar kula da kafofin yaɗa labarai ta ƙasa, NBC, ce kaɗai ke da ikon rufe kafofin.

A kwamashinan, majalisar ta kuma umarci kwamashinan ‘yan sanda da ya kama dukkan ‘yan jaridar da suka halarci taron wanda ɗan takarar gwamna na PDP, Dauda Lawal Dare, ya shirya.

Tun farko gwamnatin Zamfara ta ba da sanarwar hana tarukan siyasa tare da ɗaukar matakan tsaro na musamman a ƙananan hukumomin Anka da Gusau da Gumi da Bukuyum – inda hare-haren ‘yan fashin daji suka fi ƙamari.

Sai dai PDP ta shirya taron a ranar Asabar da zimmar karɓar wasu ‘yan adawa da suka sauya sheƙa zuwa jam’iyyar tasu, har ma rahotanni suka ce an samu hatsaniya tsakaninsu da ‘yan jam’iyyar APC mai mulkin jihar.

natforce 
latest news today

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Peter Obi na nan a cikin jam’iyyar har yanzu – LP

Shugaban ƙungiyar Obidient Movement, Dr. Tanko Yunusa ya ce...

Yadda Mahara sun kashe mutum biyu, sun ƙona gidaje a Filato

Wasu da ake zargin mahara sun afka wa karamar...

An YI zanga-zanga a Isra’ila kan shirin Netanyahu na mamaye Gaza

Dubban mutane sun fito kan tituna a faɗin Isra'ila,...

Birtaniya za ta fara tisa ƙeyar bakin da suka aikata laifi zuwa kasarsu

Birtaniya ta fitar da sabon tsarin tisa keyar duk...

NDLEA ta kama Fasto kan zargin safarar miyagun ƙwayoyi

Hukumar hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi ta Najeriya,...

Gwamnoni sun mika sakon ta’azziya ga iyalan Audu Ogbeh

Shugaban ƙungiyar gwamnonin arewa kuma gwamnan jihar Gombe, Muhammadu...

Duk wahala sai dai mu mutu a Gaza – Fatma

Wata mai mai ƴaƴa tara ta ce, duk runtsi...

Gwamnan Kano ya kori mataimansa na musamman kan belin Danwawu

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya amince da...

Tsohon Minista a mulkin Buhari ya mutu

Allah ya yi wa tsohon ministan noma da raya...

Kashi 70 na yankin Bukuyum ta Kudu na ƙarƙashin ƴan Bindiga – Ɗan majalisa

Rahotanni daga yakin ƙaramar hukummar Bukuyum na jihar Zamfara...

Goodluck ya fi dacewa ya zama dan takara a 2027 – Lamido

Tsohon Gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido ya ce Tsohon...

An gargadi al’umma su yi taka tsan-tsan da ambaliyar ruwan sama

Yayin da ake ci gaba da fuskantar saukar ruwan...
X whatsapp