fidelitybank

Gwamnatin Zamfara ta amince da albashin dubu 30 ga ma’aikata

Date:

Gwamnatin jihar Zamfara, ta amince ta aiwatar da mafi karancin albashin naira dubu 30 ga ma’aikatan jihar.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwar da babban daraktan yada labarai na ofishin mataimakin gwamna, Babangida Umar, ya fitar ranar Laraba a Gusau, babban birnin jihar.

Mataimakin gwamna, Sanata Hassan Nasiha, ya sanar da hakan ne yayin karbar takardar yarjejeniyar da gwamnati ta kulla da ma’aikatan.

Mataimakin gwamnan ya nuna jin dadinsa game da yadda kungiyar kwadago ta nuna girma da fahimta yayin yarjejeniya da ma’aikatan gwamnati.

Fahimtarsu ta sa aka yanke shawarar aiwatar da mafi karancin albashi na N30,000 a watan Nuwamba.

“Halin da ake ciki na tabarbarewar tattalin arziki da kalubalen tsaro na cikin abubuwan da gwamnati ta yi la’akari da su kafin ta amince da aiwatar da sabon albashin,” in ji shi.

Ya kuma yaba wa kwamitin da Ambasada Bashir Yuguda ya jagoranta da ya wakilci gwamnati wajen cimma matsaya da kungiyoyin kwadago cikin lumana.

vanguard news

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Barrister Sa’idu ya kama aiki bayan ya maye gurbin Muhyi Magaji

Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya rantsar...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

An ceto Mutane 26 da kwale-kwale ya kife da su a Sokoto

An samu nasarar ceto mutum 29 bayan hatsarin kwale-kwale...

Barau zai mayar da filin wasan BUK na zamani

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau I. Jibrin, ya...

Jami’ar Bayero ta Kano ta yi sabon shugaba

Farfesa Haruna Musa, ya karɓi ragamar shugabancin jami’ar Bayero...

Gwamnatin Kano ta amince Barau FC ta yi wasa a filin Sani Abacha

Gwamnatin Jihar Kano ta amince da kungiyar kwallon kafa...

Gwamnatin Tinubu na takalar Kwankwaso da fada – Buba Galadima

Jigo a jam'iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan...

Newcastle United ta dauki dan wasan tsakiya Jacob daga Aston Villa

Newcastle United ta sanar da daukar dan wasan tsakiya...

Hisba ta kama ‘yan Mata 62 da zargin aikata baɗala a Kano

Hukumar Hisbah ta kama mutane 62 kan zargin aikata...

NNPP ta yi tafka magudi a zabencike gurbin Kano – Farouk Lawan

Tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya yi zargin...

Dan shugaban kungiyar Boko Haram ya shiga hannu

Hukumomi a ƙasar Chadi sun kama yaron shugaban ƙungiyar...
X whatsapp