fidelitybank

Gwamnatin Tinubu za ta fara ciyar da Ɗalibai

Date:

Gwamnatin tarayya ta sanar da cewa, za ta sake kaddamar da shirin ciyar da ɗalibai a makarantu, ranar 29 ga watan Mayu.

Ƙaramin Ministan ma’aikatar jin-ƙai da rage talauci, Dr Yusuf Sununu ne ya bayyana hakan a ranar Larabar da ta gabata yayin wata ganawa da ƙungiyoyi masu zaman kansu da kuma jami’an gwamnati a Abuja.

Sununu ya sanar da cewa za a sake kaddamar da shirin ne domin murnar cikar shugaba Bola Tinubu shekara ta biyu akan karagar mulki.

Ya ce, shirin na da nufin magance yunwa da kuma inganta ɓangaren ilimi a faɗin ƙasar baki ɗaya.

”Shirin na nufin amfanar yara miliyan 10 kuma zai iya ƙara yawan yaran da ke shiga makarantu da kashi 20 cikin 100, sannan kuma ya bunƙasa hazaƙar yara a ɓangaren karatu da kashi 15 cikin 100 ,” in ji shi.

Sake ƙaddamar da shirin na zuwa ne a daidai lokacin da ake hasashen cewa sama da ƴan Najeriya miliyan 30 na iya fuskantar matsananciyar yunwa, wanda hakan ke nuni da muhimmancin ɓullo da shirye-shirye makamantan wannan cikin gaggawa.

legit com

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Gwamnatin Tinubu ta kama-karya ce – Atiku

Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya ce, hare-haren...

An gayyaci El-Rufa’i ka n zargin tayar da rikici a Kaduna

Rundunar ƴansandan jihar Kaduna, sun buƙaci tsohon gwamnan jihar...

Badakalar Naira biliyan 1.17 ta sake kunno kai a gwamnatin Kano

Rikicin rashawa da ya dabaibaye gwamnatin jihar Kano ya...

Ba za mu daga kafa ga duk wanda ya takale mu ba – China

Shugaba Xi Jinping na China, ya ce babu wani...

Nigeria Air ba na bogi ba ne – Hadi Sirika

Tsohon Ministan sufurin jiragen sama na Najeriya, Hadi Sirika,...

Amurka ta mika wa Najeriya tallafin abinci miliyan 32.5

Gwamnatin Amurka ta bayar da tallafin dala miliyan 32.5...

Gwamnatin Kano ta gargadi kungiyar ACF

Gwamnatin jihar Kano ta gargaɗi ƙungiyar Arewa Consultative Forum...

Operation Kukan Kura ya yi aiki sosai a Kano – CP Bakori

Hukumar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta kaddamar da...

An sanya dokar ta bace a Makabartun Kano

Shugaban ƙaramar hukumar Nassarawa a Kano Honarabul. Yusuf Shuaibu...

An ga ‘Yar shekara 13 Fatima a rataye a Kano

Iyaye da sauran ‘yan uwa na cikin juyayi kan...

‘Yansanda sun kama Linga da Guchi rikakkun ‘yan Daba a Kano

Rundunar ’yan sandan jihar Kano ta kama Mohammed Isma’il...

Tinubu ya sauka da kwari bayan ya dawo daga Brazil

Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya koma Najeriya bayan kammala...
X whatsapp