Mataimakin shugaban kasa mai jiran gado, Kashim Shettima, ya bayyana cewa batutuwan da suka shafi jinsi za su samu fifiko a karkashin gwamnatin zababben shugaban kasa Bola Tinubu.
Shettima ya yi magana ne a lokacin kaddamar da litafi mai suna “Stepping on Toes, My Odyssey at Nigerian Ports Authority (NPA)” wadda tsohuwar Manajan Darakta Hadiza Usman ta wallafa.
A wajen taron da aka gudanar a ranar Asabar a Abuja, ta bayyana Hadiza a matsayin macen karfe saboda “Bajintar rubuta irin wannan littafi”.
Da yake ambaton wata shahararriyar magana a tsakanin mutane, Shettima ya ce: “Idan ka ilimantar da mace, ka ilmantar da al’umma”.
“Ka tabbatar da cewa gwamnatin Asiwaju Bola Tinubu mai zuwa za ta kasance mai son jinsi,” NAN ta ruwaito dan majalisar.
Jigon jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya tuna cewa Tinubu ne gwamna na farko da ya nada mace a matsayin mataimakiyarsa.
Shettima ya kuma tunatar da jama’a cewa, Tinubu ne ya fara nada mace a matsayin Babban Alkalin Jihar.