Ministan Lafiya na Najeriya Ali Pate ya ce gwamnatin tarayya na duba yiwuwar fara aiki da mutum 28,000, waɗanda a baya ke aiki da hukumar ba da agaji ta Amurka United States Agency for International Development (USAID).
Da yake magana yayin wata hira da gidan talabijin na Channels TV ranar Juma’a, ministan ya ce gwamnatin tarayya na da niyyar gyara ɓangaren kiwon lafiyar ƙasar yayin da Amurkar ke janye tallafin da take bayarwa ta hannun USAID.
Bayan hawansa mulki ne Shugaban Amurka Donald Truymp ya umarci a dakatar da bayar da tallafi wajen samar da magunguna da ayyuka kamar na cutar HIV a ƙasashe masu tasowa har sai an kammala bincike kan lamarin.
Ministan ya ƙara da cewa Najeriya ba ta zuba kuɗaɗe masu yawa ba a ɓangaren lafiyar, yana mai cewa Shugaba Bola Tinubu “a shirye yake wajen sauya alƙiblar tsarin”.
Ya ƙara da cewa fiye da kashi 70 na magungunan da ake amfani da su a Najeirya daga waje ake shiga da su ƙasar.