fidelitybank

Gwamnatin Tinubu ta ayyana dokar ta ɓace a kan matsalar wutar lantarkin Arewa – Ƙungiyar Dattawan Arewa

Date:

Kungiyar tuntubar juna ta dattawan Arewacin ƙasar nan ACF, ta yi kira ga gwamnatin tarayya da ta ayyana dokar ta-ɓaci kan ɓangaren wutar lantarki a daidai lokacin da yankin arewacin ƙasar ke ci gaba da kasancewa cikin duhu sakamakon rashin wuta.

Wata sanarwa da jami’in hulɗa da jama’a na ƙasa na ƙungiyar, Tukur Muhammad-Baba ya fitar, ta yi zargin cewa dagan-gan gwamnati ta banzatar da harkar lantarki a yankin domin ƙara jefa harkokin kasuwanci cikin matsi.

ACF ta bayyana mamakin cewa me ya sa arewa wadda ke samar da wutar lantarki mai yawa a ƙasar, amma kuma a ke kasawa a ba ta kaɗan.

“Cikin mako ɗaya da ya gabata, sassan jihohin arewacin Najeriya da dama na fuskantar matsalar rashin wutar lantarki, abin da ya janyo harkokin kasuwanci da na yau da kullum suka kusa durkushewa, ga kuma ƙaruwar ɓacin-rai tsakanin al’umma,” in ji ƙungiyar.

ACF ta ce abin yana tayar da hankali matuka duba da irin sanarwa da kamfanin rarraba wutar lantarki a Najeriya (TCN) ya fitar cewa za a ci gaba da fuskantar matsalar saboda matsalolin tsaro da ake fama da su.

Ta ce bai kamata a ce jihar Legas kaɗai tana da ƙananan tashoshin samar da lantarki har guda takwas ba yayin da ɗaukacin jihohin arewa, waɗanda ke da sama da rabin al’ummar Najeriya ke da tashoshi guda uku kaɗai a Jos da Kaduna da kuma Kano.

Ƙungiyar ta yi gargaɗin cewa lamarin babbar barazana ce ga tsaron ƙasar.

Don haka ta yi kira ga gwamnatin tarayya da sauran hukumomi da abin ya shafa da su gaggauta ayyana dokar ta-ɓaci kan matslar ta rashin lantarki, kafin matsalar ra rikiɗe zuwa tashin hankali.

latest nigeria newstoday

Subscribe to Our VIP Newsletter

[newsletter_signup_form id=1]

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here

Share post:

Popular

More like this
Related

Ƴan Jagaliya sun caka wa Matashi kuwa lokacin da ya zo karɓar naman Sallah a Kano

Matashi Ibrahim Mahmud ya rasu sakamakon caka masa wuƙa...

Kallo Ya Koma Sama: Elon Musk zai fuskanci mummunar sakamako – Trump

Ana ci gaba da takun saka tsakanin shugaban Amurka...

Zulum ya miƙa kyautar Naira miliyan 100 ga iyalan Sojojin da aka kashe

Gwamna Babagana Umara Zulum na jihar Borno, ya bai...

Otal ɗin ƴan Najeriya ya kama da wuta wani ɓangaren a Saudiyya

Hukumar Alhazai ta Najeriya ta ce an samu tashin...

An kai hari maɓoyar Boko Haram a Borno

Biyo bayan sahihan bayanan sirri da aka samu, rundunar...

Alaƙar Trump da Elon Musk ta yi tsami sosai

Attajirin da ya fi kowa arziki a duniya, Elon...

An yi jana’izar Muhammad Uwais

An gudanar da jana'izar tsohon alkalin alkalan Najeriya, mai...

Musulman Nijeriya a cigaba da jajircewa – Obi

Ɗan takarar shugaban ƙasa a karkarshin jam'iyyar Labour a...

Akwai takaici ambaliyar Neja – IBB

Tsohon shugaban ƙasa, Janar Ibrahim Babangida, ya kwatanta ambaliyar...

Farfesa Jibril Aminu ya rasu ya na da shekaru 86

Allah ya yi wa Farfesa Jibril Aminu mai shekara...

Alhajin Najeriya ya rasu a tsayuwar Arfa

Wani Alhaji daga Najeriya ya rasu a filin Arfa...

Alhazai miliyan 1.673,230 ne ke gudanar da akin Hajji – GASTAT

Hukumar tattara alƙaluma ta Saudiyya (GASTAT) ta ce, Alhazai...
X whatsapp