Jigo a jam’iyyar NNPP, kuma na hannun tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Buba Galadima ya ce zai yi wahalar gaske Kwankwaso ya haɗa hannu da jam’iyyar APC domin samun nasarar Bola Tinubu a babban zaɓen shekarar 2027.
Buba Galadima ya bayyana haka ne a tattaunawarsa da tashar Channels a shirinta na Politics Today wanda aka yi a ranar Litinin, inda ya ce, gwamnatin Tinubu tana takalar Kwankwaso, musamman wajen goyon bayan Sarki Aminu Ado Bayero, duk da gwamnatin jihar ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta cire shi.