Ministan yaɗa labarai Mohammed Idris, ya ce, a daidai lokacin da gwamnatin Shugaba Tinubu ke martaba ƴancin ƴanƙasa na gudanar da zanga-zangar lumana, gwamnatin ta ƙudiri aniyar hakan bai take haƙƙin sauran ‘yanƙasa ba.
Mohammed Idris ya ce suna da bayanan da ke nuna cewa wasu ɓata-gari na da niyyar fakewa da zanga-zangar wajen tayar da fitina.
“Shugaban ƙasa ba shi adawa da zanga-zanga, kawai dai yana ƙin tashin hankali da kuma duk wani abu da zai tauye walwalar ‘yan Najeriya,” a cewarsa lokacin da yake karɓar baƙuncin ƙungiyar bishop-bishop ta Charismatic Bishop Conference a ofishinsa da ke Abuja yau Laraba.
“Ya yarda cewa kowa na da ‘yancin yin duk wani abu da bai saɓa doka ba kamar yadda dimokuraɗiyya ta tanada matuƙar dai ba a tauye wa wani haƙƙinsa ba.”
A jiya Sufeto Janar na ‘Yansanda Kayode Egbetokun ya ce za su bai wa masu zanga-zangar kariya “matuƙar dai ta lumana ce”, amma ba za su bari “mutane su ƙona gine-gine ba da sunan zanga-zanga”.
Matasa a Najeriya na cigaba da tattauna batun zanga-zangar da suke cewa za a fara daga 1 ga watan Agusta domin nuna fushinsu game da tsadar rayuwa da ake fama da ita a ƙasar.


