Gwamnatin tarayya za ta kaddamar da noman rani na wannan shekara a Hadejia da ke jihar Jigawa.
Cikin wata sanarwa da ma’aikatar albarkatun noma da samar da abinci ta kasa, ta fitar ta ce mataki wani bangare ne na kokarin kawar da tsadar abinci a fadin kasar.
A cikin watan Yuli ne shugaban kasar Bola Tinubu ya ayyana dokar ta-baci kan samar da abinci a fadin Najeriya.
Ministan harkokin noma da samar da abinci na kasar Sanata Abubakar Kyari ne zai jagoranci masu ruwa da tsaki zuwa garin Hadejia a jihar Jigawa domin kaddamar da aikin a ranar Asabar 25 ga watan Nuwamba, kamar yadda sanarwar ta bayyana.
Sanarwar ta ce za a bai wa manoma kayyakin aikin noma da suka kunshi iri da takin zamani da magungunan feshi a lokacin bikin.
Tuni dai gwamnatin kasar ta ce ta yi rangwamen kayayyakin aikin noma da kashi 50
Ana sa ran gudanar da noman ranin a duka jihohin kasar 36 da Abuja.
Inda ake ra san shuka alkamar – da aka shigo da irinta daga Mexico – da shinkafa, da masara da dawa da waken suya da kuma rogo.
Kamfanonin sarrafa fulawa hudu ne suka bayyana aniyarsu na sayen alkamar daga wajen manoman.
Ministan albarkatun noman ya bayyana kaddamar da shirin da cewa wani gagarumin ci gaba, a yunkurin da gwamnatin kasar ke yi na burin inganta kasar.
Ya kara da cewa samar da kayayyakin aikin noma da na’urorin zamani za su taimaka wajen habaka harkokin noma a fadin Najeriya.